Yunkurin agazawa ′yankin Diffa | Zamantakewa | DW | 21.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yunkurin agazawa 'yankin Diffa

A Jamhuriyar Nijer wani sabon hadin gwiwar matasan da suka fito daga bangarori daban-daban ne suka kaddamar da gidauniya domin nemo tallafin don agazawa al’ummar yankin Diffa masu fama da matsaloli barkatai

Da tsarin mai suna DIFFA I CAIRE da kuma aka fassara daga wasu harsuna na cikin gida kamar Gakasiney ko Agaji matasan da suka fito daga kungiyoyi daban-daban, na son ne a cimma wani burin kawo na su dauki daga al’umma zuwa ga wasu al’ummar da kuma ke wani bangare na kasar da ke fuskantar matsaloli kala-kala.

Malama Mariama Ibrahim Dante, na daya daga cikin matasan da suka kafa wannan kwamitin kuma ta fada wa DW cewa. 

"Burinmu shi ne mu taimaka wa yan uwanmu na Diffa da ke cikin wani matsatsi na rayuwa mai tausayi, mai daukar hankali. Suna bukatar taimako, a taimaka masu don sun a bukatar hakan ga shi ba su yi noma ba, ba kasuwanci, ga rani yana shigowa kuma ga su babu duk wata sana’a ta neman kudi ko neman wani abun kyautatawa rayuwarsu. Mu matasa muna da matakin taimaka masu domin muna da yawa a duk a binda muka saka hannunmu zai iya samun ci gaba,

To ko cikin wane hali al’ummar ta yankin Diffa ta ke ciki a halin yanzu? tambayar kenan da DW ta yi wa dan majalisar dokoki yankin Mahamane Boulou mai wakiltar Diffa a majalisar dokoki jamhuriyar Nijar, wanda kuma ya kammala aikin kai ziyarar ganewa ido da sunan majalisar dokoki a yankin a karshen makon jiya.

"Alhamdulillahi an samu sauki, amma rayuwarsu na cikin wahala suna son a kama masu. Na daya su yi sana’a na biyu su dawo a gida kamar yadda matasan su ke son kamawa Diffa, to kamata ya yi gwamnati ta tashi tsaye ta yi nata taimako to amma ta kara.

Tuni kwamitin yace ya kafa rassan sa a ko'ina cikin fadin kasar da ma kasashen waje, don kara baiwa jama’a azamar kawo nasu tallafi. Tun kafin kaddamar da kidauniyar dai kungiyoyin agajin gaggawa na gida da na kasashen waje sun ambaci neman agaji ga jama’ar yankin Diffa, da suka kiyasta sama da kashi biyu na adadin mutun miliyan daya da rabi da ke bukatar taimakon agaji a yankin na Diffa,