Yunƙurin kifar da gwamnatin Madagaska | Labarai | DW | 17.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunƙurin kifar da gwamnatin Madagaska

Sojoji masu bore sun yi yunƙurin kifar da gwamnati a Madagaska, amma bai yi nassara ba.

default

Sojojin ƙasar Madagaska, tsaye gaban tutar ƙasar su.

A ƙasar Madagaska akwai rohotonni dake karo da juna, inda wasu sojoji suka yi iƙirarin kifar da gwamnati mai ci. Wani kanal mai suna Charles Andrianasoavina, wanda ya yi magana a ta bakin sojojin da suka yi boren, ya shaida wa manema labarai a wani bariki dake kusa da filin jiragen saman ƙasar cewa, za su kafa gwamnati mai adalci. Wasu sojoji kimanin 20 ƙarƙashin jagorancin wani janar da aka kora, suka ce yanzu su ke iko a ƙasar, kuma sun dakatar da gwamnati mai ci. Sai dai shugaba Rajoelina da sauran sojojin da ke masa biyayya, sun yi alƙawarin murƙushe dakarun da suka yi boren. Wannan labarin na yunƙurin juyin mulki a ƙasar ta Madagaska, ya zo ne a dai dai lokacin da 'yan ƙasar suka jefa ƙuri'ar jin ra'ayi kan kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda zai baiwa shugaba mai ci damar ci gaba da mulki har sai an yi wani sabon zaɓe. Da ma dai janar din da ya jagoranci yunƙurin kifar da gwamnatin, shine kuma wanda ya taka rawa wajen dora shuga mai ci Rajoelina kan karagar mulki, bayan da suka kawar da tsohon shugaban ƙasar wanda shi ma ya nemi yin tazarce. Yanzu dai babu tabbas na halinda ake ciki a ƙasar, to amma a zarihiri take wani yamutsi ya faru.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala