Yunƙurin juyin mulki a ƙasar Phillipines | Labarai | DW | 24.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunƙurin juyin mulki a ƙasar Phillipines

Shugabar ƙasar Phillipines Gloria Aroyo, ta kafa dokar ta bace a faɗin ƙasar baki ɗaya, a sakamakon yunƙurin juyin mulki, da wasu sojoji su ka shirya domin kifar da ita.

A duk tsawon makon da damu ke ciki, an ta yi jita jitan shirya wannan juyi mulki, a yayin da al´ummmar ƙasar ke tunni da cikwan shekaru 10, da hambarra da shugaban yan mulkin kama karya Ferdinand Markos.

A ciki jawabin da ta yi, ta kafofin sadarwa shugabar ta bayyana wa al´umma dalilan kafa wannna doka, ta kuma umurci jami´an tsaro masu biyyaya ga gwamnati su ɗauki mattakan da su ka wajabta, don maido doka da oda a cikin kasa.

Ya zuwa yanzu, an kama Janar Danilo Lim, shugaban rundunar ƙundumballa ta ƙasa, da kalan Ariel Quevedo.

Kazalika, a na tsare da shugaban rundunar yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike, domin capke duk, wanda a ka samu da hannu, a cikin wannan yunƙuri, inji shugaba Arroyo.