Yunƙurin juyin mulki a ƙasar Cadi | Siyasa | DW | 16.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunƙurin juyin mulki a ƙasar Cadi

Gwamnatin ƙasar Cadi ta ba da sanarwar cewa, wasu masu adawa da ita, sun yunƙuri hamaɓarad da shugaba Idris Derby, ta hanyar harbe jirgin samansa yayin dawowarsa gida daga wata ziyarar da ya kai a ƙasar Equatorial Guinea.

Shugaba Idris Derby

Shugaba Idris Derby

Bisa cewar hukumomin Cadin dai, jami’an tsaron ƙasar sun murƙusad da wani yunƙurin hamaɓarad da gwamnatin shugaba Idris Derby da wasu masu adawa da ita suka yi, inda suka tanadi harbe jirgin samansa, a lokacin dawowarsa gida daga taron ƙolin shugabannin ƙasashen yankin tsakiyar Afirka da aka gudanar a ƙasar Equatorial Guinea.

A wani taron maneman labarai da ya kira a birnin N’djamena, ministan sadaswa na ƙasar Cadin, Hourmadji Moussa Doumgor, ya bayyana cewa, an murƙusad da yunƙurin juyin mulkin ne tsakanin ran talata da rana da jiya laraba, wato ranar dawowar shugaban Derby daga taron kolin na Equatorial Guinea.

Ministan ya ƙara da cewa, madugan juyin mulkin sun haɗa ne da wasu `yan kusa da shugaban, waɗanda a da ke riƙe da muhimman muƙamai cikin manyan jami’ansa fararen hula. Ya dai ambaci sunan Tom da Timane Erdimi, wasu `yan biyu, waɗanda ke da dangantakar `yan uwanci ma da shugaban, amma waɗanda a cikin watan Disamban bara, suka canza sheƙa suka koma sansanin `yan zaman gudun hijira a ƙetare, masu adawa da gwamnatin kasar. Akwai kuma wani tsohon babban hafsan soji, wato Janar Seby Aguid, wanda shi ma ya koma ɓangaren `yan adawan a cikin watan Fabrairu, wanda kuma ke da hannu a yunƙurin juyin mulkin, inji ministan.

Ya ƙara da cewa, tuni dai an kafa wani kwamitin alƙalai da jami’an tsaro don su binciki lamarin su kuma kame duk masu hannu a yunkurin kifad da gwamnatin.

Rahotanni dai sun ce jami’an tsaro cikin ɗamarar yaƙi sun yi ta sintiri a kan titunan birnin N’djamena tun ba da sanarwar yunƙurin juyin mulkin jiya. Kazalika kuma, an katse duk layukan tarho, musamman ma dai na tafi da gidanka ko kuma salula a duk fadin ƙasar, sai dai ba a ji wani amo na bindigogi ba a duk tswaon daren jiya.

A halin da ake ciki dai, Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU ta yi kakkausar suka ga yunƙurin juyin mulkin a ƙasar Cadi. A cikin wata sanarwa, shugaban hukumar Ƙungiyar, Alpha Oumar Konare, ya yi kira ga `yan siyasar ƙasar Cadin da su warware matsalarsu cikin kwanciyar hankali ta hanyar tuntuɓar juna da kuma mai da hankalinsu kan inganta tafarkin dimukraɗiyya a ƙasar.

Su dai mahukuntan Cadin, na zargin mawabciyar ƙasar, wato Sudan ne da ɗaure wa masu adawa da su gindi. Amma su mahukuntan birnin Khartoum kuma, na watsi da wannan zargin. An dai yi ta samun tsanantar adawa ga gwamnatin shugaba Derbyn a kwanakin bayan nan.

Ta hanyar juyin mulkin ne dai shugaba Derbyn, wanda shi ma tsohon madugun `yan tawaye ne, ya hau karagar mulkin kasar Cadin a cikin watan Disamban shekara ta 1990. Bayan shekaru shida ne kuma, aka gudanad da farkon zaɓen dimukraɗiyya a ƙasar, tun da ta sami `yancinta daga Faransa a cikin shekarar 1960. Shugaba Derby ne dai, kamar yadda aka zata, ya lashe wannan zaɓen.

A cikin shekara ta 2001, a yaƙin neman zaɓe, shugaba Derbyn ya lashi takobin sauka daga muƙamminsa bayan cikar wa’adinsa na biyu. Amma bayan kwaskwarimar da aka yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar, shugaban ya amsa kiran da jam’iyyarsa ta MPS ta yi na naɗa shi ɗan takararta a zaɓen da za a gudanar a cikin watan Mayu mai zuwa.

To wannan shirin ta zarcen na ɗaya daga cikin dalilan da suka janyo hauhawar tsamari a ƙasar, inda `yan tawayen suka haɗe suka kafa wata ƙungiya a gabashin ƙasar, kusa da iyaka da Suda, wadda suka yi wa suna SCUD a taƙaice. Burinsu ne samad da sauyi da haɗin kai da dimukraɗiyya a ƙasar Cadin.