Yunƙurin 'yanto wani Bafaranse a Mali
July 24, 2010Ƙasar Faransa na ƙoƙarin ƙara matsa ƙaimi domin yin belin wani ɗan ƙasar ta da reshen ƙungiyar Alƙaida na Aqmi ya ke yin garkuwa da shi a ƙasar Mali.
Mutuman mai sunan Michel Germaneau da aka sace a Niger a cikin watan Afrilu ɗan shekaru 78 na gudanar da ayyukan agaji ne a ƙasar Mali.
Wasu rahotannin da ba a tabbatar da gaskiyarsu ba, sun ce yanzu haka ana can ana ci-gaba da yin ɗauki ba daɗi tsakanin 'yan ta'addar da kuma wasu sojojin ƙawance na ƙasashen yankin Hamada da ke samun goyon bayan ƙasashen Faransa da Amurka.
A wani farmakin dai da sojojin ƙasar Moritaniya suka kai a ranar Alhamis da ta gabata kan 'yan ƙungiyar na Aqmi, sun kashe mutane shidda kana kuma suka raunata wasu daga cikin 'yan ƙungiyar da suka samu arcewa.
Mawallafi: Abdurrahmane Hassane
Edita: Mohammad Nasiru Awal