Yunƙurin warware rikici da 'yan tawayen Sudan
June 6, 2010Shugaban ƙasar Sudan ya gargaɗin 'yan tawayen ƙasarsa da guje ma amfni da tsinin bingida wajen tayar da zaune tsaye a wannan yanki na ƙasar. A lokacin da yake jawabi a taron da jam'iyarsa ta shirya, Al Bashir ya ce ƙasarsa ta juya babbin faɗace-faɗace da juna. A maimakon haka ta rungumi tafarkin demokaradiya.
Shugaba Al Bashir ya kuma nunar da cewa tattaunar da za ta guda a yau lahadi a birnin Doha na Qatar, shi ne zai zama na ƙarshe a yunƙurin sasantawa da ɓangarorin ƙasar da gwamantinsa ke yi. Rarrabuwan kawunan da ake fiskanta tsakanin shugabanni ƙungiyoyin tawaye -na daga cikin al'amura da suka haifar da tafiyar hawainiya a tattaunawa da suka gudana a ƙasashen Tchadi da Nigeria da Lybia da kuma Qatar.
ƙungiyoyin 'yan tawaye da suka fi tasiri a Sudan wato JEM da kuma SLA sun sanar da aniyarsu na ƙaurace ma tattaunawar ta Doha.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu