1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunƙurin juyin mulki a Thailand

September 19, 2006
https://p.dw.com/p/Buiw

A ƙasar Thailand Sojoji sun yi yunƙurin hamɓara da Praminista Thaksin Shinawatra, a yayin da ya ke halartar taron Majalisar Dinkin Dunia a birnin New York.

Rahotani daga Bangkok baban birnin kasar, sun ce sojoji ne masu biyya ga wani baban jami´in soja, da a hida su ka kitsa juyin mulkin.

Saidai sanarwa daga fadar mataimakin Praminista Surakiart Sathirathai ta nunar da cewa komai ya dawo cikin hanun sojoji masu biyyaya ga gwamnati.