1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yudhayono shine ke kan gaba a zaben da aka gudanar na kasar Indonesia---

Jamilu SaniSeptember 22, 2004

Cibiyar sanya iddo ta tsohon shugaban Amurka Jimmy Cater ta ce an gudanar da zaben kasar Indonesia cikin lumana---

https://p.dw.com/p/BvgH
Hoto: AP

Tsohon janar din sojin kasar Indonesia Susilo Bambang Yuhoyono da ya tsaya takarar shugaban kasa da shugabar kasar Indonesia mai ci a yanzu Megawati Sukarnoputri shike kann gaba a kirgar kuriun da ake cigaba da yi yau larabata a zaben shugaban kasar da aka gudanar zagaye na biyu ranar litinin din data gabata.

Cikin kuriu miliyan 101 da aka kirga tun daga ranar aka gudanar da zabe izuwa yau,Yudhayono ya sami kusan kuri’u miliyan 62 cikin kuriun da alumar kasar Indonesia kimanin miliyan 123 suka kada masa lokacin zabe,inda hakan ke nuni da cewar tsohon janar din sojin kasar ta Indonesia shine ya sami gagarumar nasara cikin kuriun da alumar Indonesia suka kada lokacin zabe.

A halin yanzu dai alkaluman hukumar zaben Indonesia sun nuna cewar Yudhayono ya sami kashi 61.1 na kuriun da aka kada,yayin da shuagba mai ci a yanzu Megawati ta sami kashi 38.9 daga cikin dari na kuriun da aka kada lokacin zabe.

Har kawo yanzu dai bai fito fili yace shine ya lashe wanan zabe ba,har sai hukumar zabe ta baiyana sakamakon zabe na karshe a ranar 4 ga watan Octoba mai zuwa.

A lokacin da yake yakin neman zabe,Yudhayono yayi alkawarin bulo da sabin manufofi da zasu taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Indonesia,yaki da karbara rasahawa da kuma matsaloli na tabarbarewar harkokin tsaro da halin yanzu suka adabi kasar ta la’akari yawan hare hare na kungiyoyin tsagerun musulmi da suka adabi kasar ta Indonesia.

Muhimin abinda ke gaban tsohon janar din sojin na Indonesia da ake sa ran zamansa shugaba na gaba,shine hada kai da mai goya masa baya Yusuf Kalla wajen kafa sabin yan majalisar gudanawar da zasu taimaka wajen cika alkawarin da yayi yayin yakin neman zabe wajen samar da sabin sauye sauye na cigaban kasa a Indonesia.

A yau laraba ne aka baiyana cewar kasuwar hada hadar kudaden ketare ta Indonesia ta kara bunkasa,a yayin masu zuba jari ke mayar da hankulan su kann wajen kafuwar sabuwar gwamnati,yayin da hanun daya kuma kafafan yadda labaru na Indonesia ke cigaba da fadin albarkacin bakin su kann yadda sabuwar gwamnati zata kasance.

A yau laraba ne dai cibiyar sanya ido ta tsohon shugaban Amurka Jimmy cater data sanya iddo kann yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar Indonesia zagaye na biyu ranar litinin data gabata,ta baiyana cewar an gudanar da zaben yadda ya kamata,tun bayan kawo karshen mulkin Suharto dan mulkin kama karya.

Tsohon janar din sojin na kasar Indonesia da ake ganin ya sami goyon bayan kasahen duniya,shine dan takarar neman kujerar mulkin Indonesia da ake ganin zai dauki matakai na kawo karshen aiyukan kungiyoyin tsagerun musulmi da aka zarga da laifin hare haren ta’adancin da suka faru a kasar ta Indonesia shekaru biyun da suka gabata.