Yiwuwar rufe sansanin Guantanamo | Labarai | DW | 22.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yiwuwar rufe sansanin Guantanamo

Gwamnatin shugaba Bush Amurka na dab da yanke hukunci kan rufe sansanin gwale-gwale na Guantanamo dake Cuba tare da mayar da waɗanda ake tsare da su a sansanin zuwa gidajen yari na soji a wasu wurare inda za su fuskanci shariá. Mai baiwa shugaba Bush shawara kan harkokin tsaro da kuma mashawartan sa game da alámuran shariá, za su gana domin tattauna batun. Shi dai sansanin na Guantanamo inda Amurka ke tsare da mutane 380 waɗanda ta ke zargin yan taádda ne ya kasance lamarin da gwamnatin ke fuskantar baƙin jini da kuma kakkausar suka a ciki da wajen kasar