1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

270310 Irak Koalitionen

March 27, 2010

Fara kokarin kafa gwamnatin haɗaka a Iraki bayan zaɓen Majalisar Wakilai

https://p.dw.com/p/MfyC
Tsohon primiya Iyad AllawiHoto: AP

Tsohon premiyan Iraki Iyad Alawi  wanda ɓangarensu ta samu rinjaye a zaɓen 'yan majalisar wakilai daya gudana, ya kaddamar da tattaunawar kafa gwamnatin haɗaka, domin mulkin wannan ƙasa da yaƙi ya ɗaiɗaita, cikin shekaru biyar masu gabatowa. Mohammad Abubakar na dauke da karin bayani.

Sakamakon karshe na zaɓen majalisar Irakin dai na nuni da cewar jami'iyyar Iraqiya ta su Allawi ta na da kujeru 91, wanda ya ɗara na su priminista Nuri al-Maliki da kujeru biyu.

Tsohon Primiya Iyad Allawi ya faɗawa taron manema labari cewar, Iraki na bukatar gwamnati mai karfi da daraja da zata yiwa al'umma aiki tare da tabbatar da zaman lafiya a fadin ƙasar baki ɗaya.Ya bayyana cewar wannan tattaunawar zata haɗar da dukkan jami'iyyun siyasa dake Irakin.

Bekanntmachung der Wahlergebnisse im Irak
Magoya bayan Iyad AllawiHoto: AP

Tuni dai manazarta suka fara tofa albarkacin bakinsu dangane da sakamakon zaɓen 'yan majalisar wakilan na Iraki, kasancewar manyan ɗarikun ƙasar guda biyu watau Sunni da da shi'a sune suka samu wakilai mafi rinjaye.

Kamar yadda Ghassan al-Attiya dake cibiyar nazarin Demokradiyya da cigaban Iraki yayi nuni dashi...

" kasancewar sune manyan ɓangarori biyu da sukayi nasara, kuma Maliki na wakiltar mafi yawan mazaɓun Shi'awa, ayayinda Allawi ya ke da goyon bayan Al'ummomin Sunni, haɗakar ɓangareorin biyu itace kaɗai mafita mafi dacewa. To sai dai bayan hakan, mun kuma yi la'akari da cewar irin tsananin ƙiyayya da rashin jituwa dake tsakanin ɓangarorin biyu na iya haifar da cikas a cimma wannan yunkuri"

Ana ganin cewar Maliki zai nemi haɗin kan jami'iyyar National Alliance da suka yi kawance a baya, wadda kuma take da tushen Shi'a, kana ta samu nasarar lashe kujeru 70 a wannan zaɓen, Sai dai al-Attiyah yayi gargaɗi dangane da wannan yunkuri.....

Der irakische Premierminister Nouri al-Maliki
Priminista Nouri al-MalikiHoto: AP

"Kafa gwamnatin haɗaka a ƙarkashin jagorancin Maliki ba tare da Allawi ba zai hairfar da ɓaraka a bangaren 'yan sunni, waɗanda za su ga tamkar anyi watsi da su ne bayan zaɓen da suka shiga, kuma hakan na nufin cigaban rigingimu. Kazalika  idan Allawi ya kafa gwamnatin haɗaka ba tare da Maliki ba, suma lardunan Shi'awa 7 da suka kaɗawa Maliki ƙuri'unsu, zasu ga cewar anci amanarsu, kana za su zaci cewar Sunni da Baath zasu sake karɓan madafan iko, wanda hakan ke nufin sabuwar ɓaraka a Iraki". 

Yanzu haka dai dole ne kuma jami'iyyar haɗakar  kurdawa ta ɗauki matsayi. Domin a shekaru biyar da suka gabata ta taimaka Maliki, sai dai bayan na dangantakasu ta fuskanci koma baya. Sai dai a yanzu haka akwai ayar tambaya dangane da ko matsayinsu zai samu ingantuwa a karkashin Allawi. Kurdawan dai na bukatar Ingantaccen lardi, ayayinda Allawi ke muradin gwamnatin tsakiya mai karfi. Ghassan al-Attiyah na cibiyar Demokraɗiyyar Irakin yana da ta cewa...

" da farko dai zai kasance abu mawuyaci wa mu Al'ummar Iraki mu cimma matsaya guda, duk da cewar  cikin shekaru bakwai da suka gabata , babu irin matsalolin da bamu gani ba, amma mun cimm nasarar kaucewa".

A yanzu haka dai ana ganin cewar Iraki ta samu haɗakar 'yan majalisa daga ɓangarori daban-daban na ƙasar waɗanda suka sha ban-ban dana baya, kuma idan suka haɗa kai domin yiwa ƙasar aiki, zasu iya samun nasarar sharewa al'ummomin Iraki hawayen da suka jima suna zubarwa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Yahouza Sadissou