Yiwuwar gudanar da zabe na gaba da wa′adi a Jamus | Siyasa | DW | 23.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yiwuwar gudanar da zabe na gaba da wa'adi a Jamus

Kowace daga cikin jam'iyyun siyasar Jamus na tattare da kwarin guiwar samun nasasar duk wani zabe na gaba da wa'adin da za a gudanar a wannan shekarar

An saurara daga bakin franz Münterfering yana mai fadin cewar wannan zaben shi ne zai tantance alkiblar da siyasar kasar ta Jamus zata fuskanta, ko zata ci gaba ne akan tsarin sakarwa da harkokin kasuwanci mara tare da ba da la’akari da makomar jin dadin rayuwar jama’a, ko kuwa za a canza alkibla ne a durfafi tsarin jari hujja tsantsa. Ita ma jam’iyyar The Greens ta bayyana kwarin guiwarta a game da zaben na gaba da wa’adi da ake shawarar gudanarwa, inda take fatan tsayar da ministan harkokin waje Joschka Fischer takarar neman mukamin shugaban gwamnati. Shi dai Fischer, wanda ake yayata jita-jitar cewa da zarar yayi asarar mukaminsa zai kakkabe hannuwansa daga al’amuran siyasa ya fito fili ya ce zai amince da wannan tayi da hannu biyu-biyu. A lokacin da yake bayani ministan harkokin wajen na Jamus Joschka Fischer karawa yayi da cewar jam’iyyarsa zata shiga yakin neman zaben tattare da kwarin guiwar ba wa marada kunya, wadanda ke kokarin sake mayar da hannun agogo baya dangane da makomar siyasar kasar Jamus. Wannan lafazin dai yana mai yin nuni ne da bude kofar yakin neman zaben tun kafin a samun tabbacin cewar za a gudanar da zaben na gaba da wa’adi. Domin kuwa shugaban kasa ne ke da ikon tsayar da shawara a game da kada wata kuri’ar kin amanna da salon kamun ludayin shugaban gwamnati, amma baki ya zo daya a tsakanin dukkannin jam’iyyun siyasar Jamus cewar hakan shi ne mafi alheri. Shugabar jam’iyyar CDU Angela Merkel na tattare da kwarin guiwar samun galabar zaben ta la’akari da gagarumar nasarar da jam’iyyarta ta cimma a zaben jihar Northrhine-Westfaliya da aka gudanar a jiya lahadi. Ta magana daya ce ta rage a game da mutumin da ke da amanna a zukatan jama’a wajen tafiyar da al’amuran kasa. To sai dai kuma kawo yanzu Edmund Stoiber, shugaban jam’iyyar CSU ta jihar Bavariya bai fito fili ya bayyana niyyarsa ta janyewa daga takara domin ba wa Angela Merkel damar tsayawa takarar zaben na gaba da wa’adi ba. An dai ji bayani daga bakinsa yana mai cewar a matsayinsa na shugaban CSU zai yi bakin kokarinsa wajen ganin ‚yan Christian Union sun cimma nasara. Kuma duk wata maganar dake akwai za a yi bitar ta dalla-dalla tsakanin CDU da CSU dake kawance da juna. A lokacin wani taro na hadin guiwa da zasu gudanar a ranar 30 ga watan mayu ne za a tsayar da shawara a hukumance a game da ba wa Angela Merkel damar tsayawa takarar zaben domin kalubalantar babban dan takarar SPD.