Yinwa ta ratsa a yankin kudancin Afrika
September 9, 2005Kungiyar bada taimakon raya kasa, ta Oxfam ta yi kira ga kasashen masu hanu da shuni, da kungiyoyin daban daban na bada agaji, da su gaggawta kai taimakon abinci a yankin kudanci Afrika, inda a kalla mutane million 10 ke fama da karancin abinci.
Kungiyar Oxfam ta gayyaci kasashen da su wa´aztu, da abinda ya wakana a Jamhuriya Niger, inda sai bayan watani 6 da kiran da gwamnati tayi, na tallafawa al´umma, kanan taimakon ya fara shiga, mussaman bayan da kafofin sadarwa su ka fara nuna hotunan mattatun dabbobi, da na yara kanana rammamu, da yinwa ta karmashe.Kuma a wannan lakoci taimakon ya yi kama da gociya bayan mari,
Oxfam ta ce ba ta kamata kasashen n masu karfin tattalinn arziki su yi kunnan uqwar shegu da billa´ijn da ke wakana ahalin yanzu a yankin kudanci Afrika.
A kalla tsabar kuddade billiar guda ne,a ke bukata, domin ceton rayukan talakawan wannan kasshe, da su ka tsinci kansu, a cikin mayuyacin hali.
A ko wace ran ata Allah, inji rahoton kungiyar Oxfam, kasashe masu ci gaban masana´antu, na ware dalla billiar guda, domin tallafawa manoman su, indan su ka amince su kebe kudin rana daya tak,na tallafin da su ke yi, ga harakokin nonam kasashen su, ya wadata,r a ceci rayukan millliyoyin jama´a nahiyar Afrika.
Idan ba a manta ba,a watan da ya gabata shugabanin kungiyar SADC da ta hada, kasashen yankin kudancin Afrika sun yi zaman taro a birnin Gaborone na Botswana inda su ka ja hankalin dunia, a game da bill´in yinwa da al´ummomin su ke fuskanta.
Saidai ya zuwa yanzu, babu ko kwandalla, da ta shiga da sunan taimako daga kasashen ketare.
Idan ba a yi ba takantsatsan an bi hanyar shiga matsayin yinwaer da ta gallabaita milliyoyin jama´a a Jamhuriya Niger.
Albarkacin wannan zaman taro, shuwagabanin sun yanke shawara game karfi, da hussa´o´i domin, daukar matakan rage raddadin matsalar, kamin a fara samun taimako daga kasashen dunia.
Sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia, Koffi Annan a wata fira da yayi da manema labarai ya tabatar da cewa, ba´ada bayan yankin Sahel, da na kudancin Afrika, Sudan,Habasha da Somalia, na daga cikin jerin kasashe da ya kamata a kaima tallafin abinci, na gaggawa, amma har yanzu Majalisar Dinkin Dunia, ta rufe ido ga matsalolin wannan kasashe.
Abinda ya fi daukar hankulla a halin da ake ciki, shine na taron Majalisar, da kuma kwaskwarimar da za ayi mata, sannan da batun yaki da ta´adanci.
A karshe, kungiyar Oxfam, a cikin wannan rahoto,ta gayaci shuwagabanin yankunan da ke fama da balla´in yinwar,, da su kara daukar matakan kulla da al´ummomin su, domin a halin yanzu,neman taimako daga ketare, ya zamma, tamkar jiran gawon shanu.