1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yini na uku a yajin aikin maaikata a Nigeria

June 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuI8

Ayayinda a yau aka shiga yini na uku da fara yajin aikin gama a tarayyar Nigeria,shugabbanin kwadago sun dada zage dantse dada jefa wannan kasa mai albarkatun man petur cikin halin kakanikayi na rayuwa,bayan gaza cimma matsaya guda a tattaunawar da suka gudanar da wakilan gwamnati,adangane da farashin mai.

Kungiyoyin kwadagon dai sunyi barazanar cigaba da yajin aikin ,wanda tuni ya durkusar da harkokin tattalin arzikin wannan kasa,zuwa kayayyakin masarufi da suka hadar da ruwan sha da wutan lantarki.

Hukumomi a Nigeriar dai sunyi ikirarain cewa bazasu cigaba da zuba idanu akan wasu halayya na yan kwadagon wanda ya sabawa dokar kasa ba ,musamman tare hanyoyi da gidajen mai da kuma musgunawa maaikata.Da asubahin yau nedai aka tashi baran baran tsakanin bangarorin biyu,inda yan kwadagon suka bukaci cire dukkan naira 10 da aka kara na farashin mai,gwamnati kuwa ta tsaya kan bakanta na cire naira biyar kachal.