Yini na biyar na kazamin fada a tsakiyar Somaliya | Labarai | DW | 24.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yini na biyar na kazamin fada a tsakiyar Somaliya

Kazamin fada na cigaba da gudana tsakanin mayakan gamayyar kungiyoyin musulmi da mayakan gwamnatin rikon kwarya na somalai,wadanda dakarun kasar Habash ke taimakawa,a tsakiyar kasar wanda ya shiga yini na biyar a yau babu kakkautawa.Wannan fada dake neman cika mako f´guda dai ya barke ne a garuruwa guda biyu dake karkashin ikon kungiyoyin musulmin.Kakakin gamayyar kungiyoyin musulmin dake garuruwa biyu Mohammed Mohamoud Jumale ya fadawa manema labaru cewa,wannan arangama na yau na mai kasancewa mafi tsanani,da barkewan wannan fada kwanaki biyar da suka gabata.Rahotanni daga Baidoa,matsugunnin gwamnatin somaliyan kuwa na nuni dacewa,an ji tashin wasu ababai dake da nasaba da boma bomai a kusa da gine ginen gwamnati dake garin,da safiyar yau.