1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yin amfani da ma'adinai tamkar makaman siyasa.

January 3, 2006

Rikicin da ya barke tsakanin Rasha da Ukraine na nuna cewa, karancin ma'adinai a duniya, zai iya zamowa tushen barkewa wasu sabbin tashe-tashen hankulla a duniya.

https://p.dw.com/p/Bu2n
Masana'antar hayakin gas a kasar Ukraine.
Masana'antar hayakin gas a kasar Ukraine.Hoto: dpa - Report

Hasashen da aka yi na samun hauhawar tsamari tsakanin Rasha da Ukraine ya tabbata: Tuni dai Rashan ta katse wa makwabciyarta hanyoyin samun makamashi na hayakin gas tun daga ranar farko ta wannan shekarar. Masharhanta da dama na ganin wannan matakin tamkar wata dabara ce ta angaza wa Ukraine din a siyasance. A cikin wannan shekarar ne kuwa, Rasha za ta karbi jagorancin rukunin nan na kasashen G-8. Amma wannan matakin da kamfanin Gazprom, wanda gwamnatin Rashan ta fi rinjayin masu zuba jari a cikinsa ya dauka, ya kasance wani abin damuwa ne ga kasashen Kungiyar Hadin Kan Turai da dama. Sai dai, manazarta al’amuran yau da kullum na ganin cewa, nuna son kai kawai kasashen yammacin Turan ke yi.

Da can ai an sha yin gangami kan karancin albarkatun kasa a duniya, ko da ruwa ne, ko gas ko man fetur da dai sauransu. Amma kasashen yamman ba su nuna damuwarsu ba. Yanzu da suke ganin rikicin hayakin gas tsakanin Rasha da Ukraine, zai iya zamowa wata barazana gare su ne suka fara gama gira, suna bayyana fargabarsu.

Rikici tsakanin Rashan da Ukraine dai, ba tun yau ake yinsa ba. An dade kasashen biyu na ta ka ce na ce kan wanda zai fi samun angizo a kan bututun makamshin da ke kai hayakìn gas zuwa yammacin Turai da kuma zargin da Rashan ke yi wa Ukraine na cewa tana sace hayakin gas din daga bututun da ke bi cikin kasarta zuwa yammacin Turai. Tun shekaru da dama ne dai Rashan ke samar wa yammacin Turai makamashin hayakin gas da take bukata. A wata ziyarar da ya kai a birnin Moscow a lokacin da yake rike da mukaminsa, tsohon shugaban kasar Jamus Roman Herzog, ya bayyana damuwarsa ta cewa, za a fa wayi gari a sami Jamus ta dogara kacokan kan samun makamshin gas da take bukata daga Rasha. Sai dai, a wannan lokacin, a cikin shekarun 1990, babu wanda ya nuna sha’awa ga batun. Rikici tsakanin Moscow da Kiew dai na nuna cewa, za a iya yin amfani da ma’adinai tamkar wani makami na cim ma burin siyasa.

Amma ko ba dade ko ba jima, za a dai warware wannan rikicin tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna. Ita Rashan ma na da sha’awar ganin cewa, an sasanta wannan rikicin. Saboda idan aka ci gaba da shi, kwarjinin Rashan a kasashen yamma zai dusashe. Manufar da shugaba Putin ya sanya a gaba, wato ta gurgunta yunkurin da Ukraine din ke yi na shiga cikin kungiyar Hadin Kan Turai, tana nuna alamun cin tura. Angaza wa kasar da Rasha ke yi ma, ta sa mahukuntan birnin Kiew na ta kara samun goyon baya daga Yamma.

Abin da ya kamata a yi la’akari da shi a nan shi ne, ba a Turai kawai ne ake sammun hauhawar tsamari game da wannan gwagwarmayar ta mallakar ma’adinai ba. Tuni dai Amirka na nuna matukar shakku ga kasashen Sin da Indiya, saboda habaka cinikin hayakin gas da suke yi da Iran. Ita dai Iran, ita ce kasa ta biyu mafi arzikin albarkatun hayakin gas a duniya. Sabili da haka ne kuwa, mahukuntan biranen New Delhi da Beijing ke watsi da duk wata damuwar da Amirkan za ta nuna game da wannan harkar da suke yi da Jumhuriyar ta Islama. Bugu da kari kuma, sai ga shi Rasha ta ce za ta ci gaba da da bunkasa ayyukan hadin gwiwa a fannin makamashin nukiliya.

Babu shakka, ko ta yaya aka dubi lamarin dai, za a ga cewa, Amirka da Yammacin Turai za su ci gaba ne da dogara da kuma samo makamshinsu daga wasu yankuna daban-daban na duniya. Fatar da duk masu son zaman lafiya cikin lumana a duniya baki daya ke yi ne dai, wannan rikicin, tsakanin Rasha da Ukraine ba zai habaka ya zamo tushen wata sabuwar annoba kuma ga bil’Adama ba.