Yemen tana cikin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 23.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yemen tana cikin tsaka mai wuya

Kimanin mutane 45 ne suka hallaka yayin wasu tagwayen hare-haren ta'addanci da aka kai a birnin Aden na kasar Yemen.

Harin IS a birnin Aden na Yemen

Harin IS a birnin Aden na Yemen

Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan IS da ke rajin kafa daular Musulunci ta dauki nauyin kai wannan hari. Harin na farko dai wani dan kunar bakin wake ne ya kai shi, inda ya tashi motarsa da ke makare da bama-bamai a kofar ofishin rundunar sojojin kasar dai dai lokacin da ake tantance sojojin da za a dauka aiki.

Hari na biyu kuwa an kai shi ne a kofar gidan wani babban jam'in tsaro, inda maharin ya tayar da bama-baman da ke daure a jikinsa cikin wasu taron sojoji da ke tsaye. A baya-bayan nan dai sojojin gwamnatin kasar da ke samun goyon bayan dakarun rundunar taron dangi wadda Saudiya ke wa jagoranci, na fuskantar hare-hare daga kungiyar 'yan ta'adda ta IS.