1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matsalar abinci a Yemen

Suleiman BabayoJune 21, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin karancin abinci da ake fuskanta a Yemen sakamakon rikice-rikice da ake fsukanta a kasar.

https://p.dw.com/p/1JArF
Jemen Der Markt in Taiz
Hoto: Getty Images/AFP/A. Al-Basha

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan yadda kimanin mutane milyan bakwai suke cikin matsananci rashin abinci a kasar Yemen, kuma tuni lamarin ya kazance. Hukumar majalisar mai kula da abinci ta bayyana haka a cikin wani rahoto da ta fitar.

Rahoton hukumar ya ce an samu karin kashi 15 cikin 100 na mutanen da suka shiga matsalar yunwa, inda aka kwatanta daga watan Yuni na shekarar da ta gabata ta 2015. Fiye da 'yan Yemen milyan biyu suka tsere daga gidajensu samakaon rikicin da kasar ta samu kanta a ciki.

Bettina Lüscher take zama mai magana da yawun hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya mai kula da abinci, wadda ta ce halin da kasar ta Yemen ke ciki na bukatar agajin gaggawa.