1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: An yi musayar fursunoni albarkacin watan azumi

Ramatu Garba Baba
May 17, 2018

Gwamnatin kasar Yemen mai fama da rikicin yaki ta yi musayar fursunoni a tsakaninta da bangaren 'yan tawaye albarkacin shigowar azumin watan Ramadan.

https://p.dw.com/p/2xrIy
Jemen Sanaa Häftlinge hinter Gittern
Hoto: Imago/Xinhua

An yi musayar fursunonin ne bayan da gwamnati ta amince da sakin mayakan Houthi su kuma suka saki mayakan da ke marawa gwamnati baya da suka kama, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta fadi a wata sanarwar da ta fidda.

A daya bangaren kuwa Kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International ta yi gargadin hadarin da Yemen ke fuskanta a sanadiyar kazancewar fada a gabashin kasar inda kungiyar ke cewa dubban mutane ke ficewa daga garin Hodeida mai mahinmanci da ke gabar teku. Kungiya ta nemi a dauki mataki don shawo kan rikicin kasar da ya daidaita miliyoyin jama'a.