1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yemen: An dakatar da kai kayan agaji

Zainab Mohammed Abubakar
January 31, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwarta dangane da 'yan kasar Yemen sama da dubu 40 da suka nemi mafaka a birnin Aden, saboda rasa matsugunnensu

https://p.dw.com/p/2rprc
Jemen Separatisten kontrollieren Interimshauptstadt Aden
Hoto: Getty Images/AFP/S. Al-Obeidi

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka da rashin iya gabatar da kayan agaji ga mabukata, tun bayan da 'yan awaren da ke yaki a kudancin kasar suka kwace madafan ikon yawancin biranen yankin.

Sakon da hukumar ta wallafa ta shafinta na Twitter na nuni da cewar, yanzu haka kayayyakin agajin da aka shirya rabawa a wannan makon na jibge a tashar jiragen ruwa na birnin Aden, bayan matakin dakatar da rarraba kayan ga mabukata.

Ita ma kungiyar nan mai taimakawa yara ta "Save the children" tilas ya sa ta dakatar da ayyukan agaji a a Aden, a wani mataki na kare jami'anta daga yakin na Yemen da yanzu ya shiga shekara ta uku babu kakkautawa.