1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawancin kasashen Turai sun nuna gamsuwa da shigar turkiyya cikin Kungiyar EU

Mansour bala BelloOctober 4, 2004

A ranar laraba kungiyar gamaiyar Turai zaa tantance ko kasar Turkiyya zata iya shiga cikin tattaunawar shiga cikin kungiyar a nan gaba

https://p.dw.com/p/Bvg1
Pm Erdogan a farkon hoto
Pm Erdogan a farkon hotoHoto: AP

A bisa cimma wamnnan mnanufar ne kuwa kasashen dake cikin kungiyar suka bayyana matsayinsu kann batun na turkiyya .Kasar nan jamus dake da a kalla turkawa sama da miliyan biyu a cikin kasar ta nuna amincewa na shiga cikin tattaunawar da kasar ta turkiyya .Tun ba yau ba gwamnatin SPd ta shugaban Gwamnatin jamus Gerhard Schrorder ke nuna gamsuwa ta yarda kasar ta turkiyya ke daukar matakai na sauye sauye a fadin kasar a wani mataki na shiga kungiyar ta Eu ..To sai dai duk da wannan mataki jamiyyar adawa ta Cdu na nuna ADAwa da shirin shigar kasar ta Turkiyya cikin kungiyar a halin yanzu ..A wamni jin raayion jamar jamusawa da aka gudanar a watan jiya ya nunar da cewa kaso 50 cikin dari na jamusawan na nem,an shigar kasar ta turkiyya cikin kungiyar na dan gajeran zango a yayin da kaso 41 ke muradin ganin cewa ta shiga cikin kungiyar baki daya ..To sai dai a daura da haka a yan kwanakin nan a wata jin raayin jamaaar kasar da aka gudanar ya nunar da cewa yawancin jamusawa na nuna adawa da shigar kasar baki daya a cikin kungiyar ta Eu ...A can Kasar Britaniya kuwa gwamnatin PM Tony Blair na muradin ganin cewa an fara wannan tattaunawa da kasar ta Turkiyya a watan Disamban wannan shekara ..To sai dai sabanin jamiyyar adawa ta nan jamus a can kasar britaniya sun yi lale marhabin da shirin na Turkiyya a cikin kungiyar ..A can Kasar faransa kuwa shugaban Kasar jak Chirak a kashin kansa na nuna goyan baya ga shirin na Turkiyya am,ma kuma yawancin jamian Gwamnatinsa na nuna adawa da shirin .To sai dai ya tabbatar da gudanar da wani jin raayin faransawa a dangane da batun kafin kasar ta turkiyya ta sami amincewar kasar ta faransa a yanzu haka.A watan jiya dai bayan gudanar da wani jin raayin jamaar kasar a faransa ya nunar da cewa kaso 56 cikin dari ne ke adawa da shirin a yayin da kaso 38 cikin dari ke nuna goyan baya ..To sai dai kimanin kaso 63 cikin dari na yan kasar ke burin ganin cewa kasar a nan gaba ta shiga cikin kungiyar amma ba yanzu ba kamar yarda kasar ta turkiyya ke muradi ..daga can kasar Italiya kuwa rahotanni nna cewa Pm kasar ya amince dari bisa dari na shiga kasar cikin kungiyar .To sai dai jamiyyar hadaka ta nuna adawa da shirin na turkiyya ..A daura da haka dai jamian fadar gwamnatin Vatican ta paparoma sun nuna adawa da wannan shirin da cewa kamata yayi kasashen dake cikijn kungiyar sufi mayar da hankali kacokam ga kasashen dake bin akidar addinin kirista .Rahotanni dai na cewa jin raayin jamaaar kasar ya nunar a fili cewa