Yawan ´yan gudun hijira ya karu a duniya baki daya | Labarai | DW | 19.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan ´yan gudun hijira ya karu a duniya baki daya

A karon farko cikin shekaru 5, a bara yawan ´yan gudun hijira a duniya baki daya ya karu matuka gaya. Babbar hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD ta ce an shiga wannan mummunan hali ne sakamakon yakin kasar Iraqi. A cikin rahotonta na shekara wanda ta bayar yau ranar ´yan gudun hijira ta duniya, hukumar ta ce tashe tashen hankula da ke kara yin muni a Iraqi ya tilastawa ´yan kasar su kimanin miliyan daya da rabi tserewa. Har yanzu dai kasar Afghanistan ce ta fi yawan ´yan gudun hijira a duniya baki daya.