Yawan waɗanda suka rasu a rushewar wata gada a China ya kai mutum 28 | Labarai | DW | 14.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan waɗanda suka rasu a rushewar wata gada a China ya kai mutum 28

Akalla mutane 28 sun rigamu gidan gaskiya yayin sama da 20 suka jikata lokacin da wata gada ta rushe a kudancin kasar China. Rahotanni na nuni da cewa mutane da dama sun bace saboda haka yawan wadanda suka mutu ka iya karuwa. Gadar wadda ake cikin aikin gina ta ta rushe ne a yankin Fenghuang dake zaman wata cibiyar ´yan yawon shakata a kasar ta China. Kamfanin dillancin labarun hukuma Xinhua ta ce har yanzu ba´a san musabbabin aukuwar hadarin ba amma jami´ai sun fara gudanar da bincike.