1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan sojojin Amirka da aka kashe a Iraqi ya tashi zuwa dubu 2.

October 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvNq

Tun da aka fara yakin Iraqi, yawan sojojin Amirka da aka kashe a wannan fafatawar, yanzu ya tashi zuwa dubu 2. Game da sabbin alkaluman da aka bugan dai, shugaba George W. Bush ya ce har ila yau yakin Iraqin zai dau tsawon lokaci kafin a gama. Sabili da haka ne kuma yake watsi da kiran da ake yi masa na ya janye dakarunsa daga kasar.

A cikin jawabin da ya yi a birnin Washington, shugaba Bush ya nanata cewa, ana samun ci gaba a huskar siyasa a Iraqin, musamman ma dai, game da amincewa da kundin tsarin mulkin da `yan kasar suka yi, abin da kuma ya share fagen gudanad da zabe a kasar a cikin watan Disamba mai zuwa.

Alabaluma dai na nuna cewa, yawan sojojin Amirka da suka ji rauni a yakin kuma, ya kai dubu 15.

kungiyoyi da dama a Amirkan dai sun ce za su yi shagulugula da dama kamarsu taron addu’a da kuma zanga-zanga, don kira ga shugaban Amirkan ya janye dakarun kasar daga Iraqi.