Yawan mutanen da suka tsere daga yakin Siriya ya haura miliyan biyar | Labarai | DW | 30.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan mutanen da suka tsere daga yakin Siriya ya haura miliyan biyar

Mafi yawansu kuwa sun tsere ne zuwa kasashen Turkiyya da Lebanon da Jordan da Iraki, sai kuma kasar Masar, inda aka yi rajistarsu a matsayin 'yan gudun hijira.

Sabbin alkalumman da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar sun nuna cewa yawan mutanen da suka tsere daga yakin kasar Siriya ya haura miliyan biyar. Mafi yawansu kuwa sun tsere ne zuwa kasashen makwabta irinsu Turkiyya da Lebanon da Jordan da Iraki, sai kuma kasar Masar, inda aka yi rajistarsu a matsayin 'yan gudun hijira. A yakin basasan da ya barke kasar shekaru shida da suka wuce, mutane kimanin dubu 400 aka kashe. A lokacin da yake gabatar da sabbin alkalumman a birnin Geneva, kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya Filippo Grandi ya ce dole gamaiyar kasa da kasa ta fadada yawan taimakon da take ba wa 'yan gudun hijirar.