Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a taɓargazar gubar masana’antu a Côte d’Ivoire ya tashi zuwa 5. | Labarai | DW | 10.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu a taɓargazar gubar masana’antu a Côte d’Ivoire ya tashi zuwa 5.

Yawan mutanen da suka rasa rayukansu, sakamakon shaƙan hayaƙin dagwalgwalar masana’antu mai guban nan a ƙasar Côte d’Ivoire, ya tashi zuwa 5. Ma’aikatar kiwon lafiyar ƙasar ce ta bayyana haka yau a birnin Abidjan, inda ta ƙara da cewa, kusan mutane dubu 6 ne suka shaƙi hayakin gubar, daga dattin masana’antun da aka jibge a wurare daban-daban a birnin, mai yawan jama’a kimanin miliyan 4.