1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yawan mutanen da suka a hadarin jirgin sama a Nijeriya ya karu

Yawan wadanda suka rasu a hadarin jirgin saman da ya auku jiya a filin jirgin saman birnin Fatakwal yanzu ya kai mutum 107, bayan wasu 4 sun cika sakamakon raunukan da suka samu. Kwamishinan ´yan sanda a birnin na Fatakwal Samuel Adetuyi ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa har yanzu dai akwai mata 3 daga cikin mutane 110 dake cikin jirgin saman samfurin DC-9 a raye, amma biyu daga cikin su na kwance a asibiti rai hannun Allah sakamakon rauni na kuna da suka samu. Daga cikin sauran mutanen da suka rigamu gaskiya a wannan hadarin dai akwai yara 71 na makarantar Loyola Jesuit College dake Abuja. Yaran dai na kan hanyar zuwa gida ne saboda hutun kirsmatti. A kuma halin da ake ciki shugaba Olusegun Obasanjo ya kira wani taron gaggawa da shugabannin kamfanonin zirga-zirgar jiragen sama da jami´an sufurin jirgin sama bayan munanan hadura 3 cikin makonni 7 da suka yi sanadiyar mutuwar mutane 224 a cikin kasar.