1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yawan Mutanen Birnin New York

Abba BashirApril 18, 2006

Birane mafiya yawan Mutane a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVW
Birnin New york
Birnin New yorkHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malama Rabi Ibrahim daga Jiddah a Makkatul-mukarramah. Malamar ta ce, kasancewar Birnin New York shine Birni mafi yawan Al’umma a Kasar Amurka,to a Duniya kuma shine na nawa a yawan al’umma?

Amsa: To malama Rabi, idan aka hada da garuruwan dake karkashinsa,Birnin New York shine Birni na biyar (5) a jerin Birane mafiya yawan al’umma a Duniya, inda ya ke da yawan al’ummar da suka kai Mutane 16,626,000.

Amma idan ana batun Birnin da ya fi kowanne Birni yawan al’umma a Duniya, to Birnin Tokyo,da ke kasar Japan, shine Birnin da ya fi kowanne yawan al’umma a Duniya, inda ya ke da yawan al’umma da suka kai Mutane Miliyan 28,025,000.

Gadai jerin Birane goma (10) wadanda suka fi yawan al’umma a Duniya.

1. Tokyo, Japan - 28,025,000
2. Mexico City, Mexico - 18,131,000
3. Mumbai, India - 18,042,000
4. Sáo Paulo, Brazil - 17, 711,000
5. New York City, USA - 16,626,000
6. Shanghai, China - 14,173,000
7. Lagos, Nigeria - 13,488,000
8. Los Angeles, USA - 13,129,000
9. Calcutta, India - 12,900,000
10. Buenos Aires, Argentina - 12,431,000

Da fatan mai sauraron tamu ta gamsu da wannan amsa.