Yawaitar mabiya addinai a Switzerland | Zamantakewa | DW | 10.07.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yawaitar mabiya addinai a Switzerland

Tun a cikin shekarun 1970 yawan addinai ke ƙaruwa a ƙasar Switzreland.

default

Allon kamfen na jam´iyar SVP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da kuma zamantakewa tsakanin al´umomi daban daban a wannan duniya ta mu.

Tun a cikin shekarun 1970 aka fara samun ƙaruwar yawan mabiya addinai daban daban musamman musulmi a ƙasar Switzerland. A halin da ake ciki yawan musulmi ya kai kashi 18 cikin 100 na yawan al´umar ƙasar ta Switzerland. An bayyana wannan ci-gaban na yawan addinai daban daban a ƙasar da cewa yana da muhimmanci a zamantakewa tsakanin al´umar ƙasar baki ɗaya. Muna ɗauke da ƙarin bayani a cikin shirin na yau.

A cikin kwanakin nan wasan ƙwallon ƙafa ya fara jan hankulan mabiya addinai daban daban a ƙasar Switzerland ɗaya daga cikin ƙasashe biyu da suka ɗauki nauyin shirya gasar cin kofin ƙwallon ƙafar nahiyar Turai da aka kammala a ƙarshen watan da ya gabata. A wani wasan ƙwallon ƙafa na sada zumunci da aka yi a birnin Bern tsakanin ´yan siyasa da wakilan addinai, tawagar addinin ne suka yi nasara da ci ɗaya da nema. Thomas Wipf na majalisar ƙungiyoyin addinai ya ba da dalilan da suka sa limaman coci da na masallatai suka shirya wannan wasa tsakaninsu da ´yan siyasa.

Wipf:

Ya ce “A Switzerland muna fuskantar ƙalubale na yawaitar mabiya addinai da al´adu waɗanda a dole su ke ba juna haɗin kai. A wani lokaci ana gudanar da zazzafar muhawwara da ke kai ga tashin hankali. Yanzu muna son aike da saƙo mai muhimmanci don samun fahimtar juna da wanzar da zaman lafiya a tsakani. Muna son a san cewa addinai suna zaman lafiya ne da juna amma ba gaba ba.”

Zama tare bisa dole ya zama muhimmin abu, domin tun a shekarun 1970 yawan addinai a Switzerland ya ƙaru, inda addinan Musulunci, Hindu da kuma Bhudda suka samu yawan mabiyansu. A ma halin da ake ciki yawan mabiya addinan Hindu da Bhudda ya fi na Yahudawa a ƙasar ta Switzerland. Alƙalumman sun yi nuni da cewa yanzu kimanin kashi 75 cikin 100 na ´yan ƙasar mabiya manyan ɗarikun Kiristoci biyu ne wato Katholika da Evangelika. A shekarar 1970 ´yan Katholika da Evangelika a ƙasar ya kai kashi 98 cikin 100. ´Yan majami´ar Evangelika musamman masu ra´ayin canji a yankunan Calvin da Zwingli a ƙasar ta Switzerland sun fi fama da koma baya a yawan mabiya ɗarikar su idan aka kwatanta da yawan masu fita daga ɗarikar Katholika. Martin Baumann masanin kimiyyar addini ne a ƙasar ya yi ƙarin bayani yana mai cewa.

Baumann:

“´Yan ra´ayin kawo canji na majami´ar Evangelika sun fi rasa magoya baya a biranen Geneva, Basel da a da suka zama sansanonisu. Sai kuma birnin Zürich da garin Zwinglis inda ake iya cewa yanzu ´yan majami´ar Katholika sun fi rinjaye. Ko da yake har yanzu masu ra´ayin sauyin na da ƙarfi a biranen amma ba kamar a shekarun baya ba.”

Kasancewar Switzerland a matsayin ƙasar da babu ruwanta ya sa ta zama wani tudun mun tsira ga masu ƙaura daga yankunan da ake fatattakarsu. Birnin Geneva da ke matsayin yankin ´yan Evangelik ya buɗe ƙofofinsa ga mabiya wannan ɗarika da suke tsere daga birnin Nantes na Faransa saboda wata doka da aka kafa. A lokacin rikicin ƙasar Hungary, Switzerland ta ba da mafaka ga ´yan ƙasar. Hatta ´yan yankin Tibet da suka tserewa tursasawa daga hukuma su ɗin ma an karɓe su hannu bibiyu. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da a yau Switzerland ta ke da gamaiyar ´yan Tibet mafi girma a nahiyar Turai. Bayan rugujewar tarayyar Yugolabiya ma Switzerland ta sake zama wani sansanin ɗaukar ´yan gudun hijira da yawa daga cikinsu mulsumi, inji Martin Baumann sannan sai ya ƙara da cewa.

“Ina ganin sassaucin ra´ayi wanda bisa al´ada ya yi tasiri a ƙasar Swizerland shi ne babban dalilin da ya sa waɗanda ake fatattakarsu daga yankunansu na asali suke samun mafaka a Switzerland ba tare da an bambamta addinisu ba, duk da adawa da haka da jam´iyun masu kishin ƙasa ke nunawa. Ƙasar ta buɗe ƙofofinta ga dukkan ´yan gudun hijira na ɓangarori daban daban. Ina ganin a dangane da wannan al´ada ya sa Switzerland ta ke tausayawa da nuna fahimta ga buɗe ƙofofinta ga waɗanda ake fatattakansu. To sai dai abin baƙin ciki shi ne yanzu ana ƙara sanyan tarnaƙi ga wannan kyakkyawar al´ada ta yin maraba da baƙin.”

Yayin da a shekarun 1960 shugabannin ke bin matakai na sassauci da maraba da sauran al´umomin duniya musamman a bukukuwan buɗe masallatai, yanzu ´yan siyasa a ƙasar ta Switzerland suna nuna fargaba ne game da sababbin ƙungiyoyin addinan da cewa sun yi yawa. Wannan matsayin a yanzu bai rasa nasaba da yawaitar masu ƙyamar baƙi da kuma gagarumar nasarar da manufar jam´iyar ´yan kishin ƙasa a Switzerland ke samu. Alal misali a bara jam´iyar kishin ƙasa ta SVP ta fara wani kamfen na hana gina masallaci mai hasumiya. A halin yanzu jam´iyar ta tattara sunayen mutane sama da dubu 100 da ake buƙata kafin a haramta gina hasumiyar masallaci a ƙasar. Jam´iyar ta SVP kuwa ta fi samun goyon bayan ne musamman a yankunan karkara inda har yanzu ake da rinjayen Kiristoci. Har yanzu wasu ´yan ƙasar sun ƙi yarda da cewa Swizterland ta zama wata ƙasa mai mabiya addinai daban daban, inji Baumann masanin kimiyar addini.

“A nan muna iya fahimtar abubuwa biyu a bayyane, wato wata al´umma wadda a da ta kasance ta turawa zalla da ke bin addini guda ɗaya ko dai ɗarikar Katholika ko kuma ɗarikar Evangelika, amma yanzu ta kyau. Na biyu shi ne an samu wasu addinan waɗanda ke jan hankulan wasu daga cikin al´ummomin ƙasar. Su ma waɗannan addinan suna son su tabbatar da matsayinsu a tsakanin jama´a. Wato ke nan yanzu ana iya cewa ba bu tsarin nan na addini guda ɗaya tilo a cikin ƙasar. Ina ganin yanzu Switzerland na cikin matakin farko a wannan sabon yanayin zamantakewa dangane da baƙi ´yan ƙaƙagida. A wannan ɓangare dai tana bayan ƙasashe kamar su Jamus da Birtaniya da shekaru barkatai.”

A farkon watan Yuni al´umar ƙasar sun nuna goyon baya ga shirin tsananta dokar ƙaƙagida. To amma ´yan jam´iyar social democrats na da niyar sauƙaƙa dokokin ba da takardun zama ɗan ƙasa. Saboda haka ya zama wajibi ´yan ƙasar ta Switzerland su kwana da sanin cewa bayan an ba da fasfuna ga sabbin ´yan ƙasar, taswirar addini a ƙasar za ta ci-gaba da sauyawa babu ƙaƙƙautawa.