Yaudara kan rikicin Palasɗinu | Siyasa | DW | 06.07.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yaudara kan rikicin Palasɗinu

Rohotonni na ƙara bayyana yadda ƙasashen Larabawa ke fakewa da rikicin Yahudawa da Palasɗinawa, inda suke tauye yancin mutanensu.

default

Amr Moussa da Khaled Meshaal

A duk lokacin da Isra'ila ta yi wa Palasɗinawa wani abu, to sai ɗaukacin larabawa su tashi suna ta ɓaɓatu, ga misali lokacin da Isra'ila ta aukawa jiragen dake kaiwa Palasɗinawan Gaza agaji, ƙasashen Larabawa sunyi ta kalaman baka. Wasu daga ƙasashen na larabawa suna anfani da abinda ke faruwa a yankin Palasɗinu domin biyan buƙatarsu kawai, bawai don tausayin Palasɗinawan ba, sai dai don siyasar cikin gida.

Tun shekaru na 1950 ƙasashen Larabawa suka mai da rikicin da suke yi da Isra'ila a matsayin abu mafi mahimmanci a rayuwarsu, wannan kuwa duk suna yi ne domin biyan buƙatunsu, inda suka manta da abubuwa masu mahimmanci kamar kare haƙƙin bil'adama da kuma wanzar da tsarin dimokraɗiyya a ƙasashensu. Sulaiman Abu Dayyeh wani ma'aikacine a cibiyar Friedrich Naumann a birnin Ƙudus.

"Tun shekarun 1990 da kuma bayan kawo ƙarshin yaƙin cacar baka, ƙasar Amirka ta ƙarfafa matsayinta a ƙasashen larabawa. Su larabawan kansu sun yi yarjeniyar zaman lafiya da Isra'ila, wasu sun sa hannu kan ƙudurori da Isra'ilan. Wannan ba saban bane ada"

Gwamnatocin Ƙasashen Jodan da Masar sun ƙulla ƙawance da Isra'ila, amma har a gobe al'ummomin ƙasashen suna matuƙar ƙin jinin Isra'ila. Sabo da har yanzu suna ganin ba'a baiwa Palasɗinawa Yancinsu ba, to amma dai gwamnatocin ƙasashen suna ɗari ɗari da sukar ƙasar ta Bani Yahudu.

A ɗaya gefen kuwa gwamnantocin ƙasashen suna amfani da batun Palasɗinawa, domin kawar da hankalin 'yan ƙasar, bisa rashin taɓuka wani abu, duk da irin arzikin mai da sauran ma'adinai da Allah ya horewa ƙasashen larabawa, idan aka ambaci ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki to larabawa suna can baya. Babu wata ƙasar Larabawa da ake zaɓen ɗemokraɗiyya, amma duk waɗannan akan shafe sune, da manufar Amirka ta yahudanci. ma'ana idan dai kana bayan Amirka to duk kashin da ka yi, sai ace yana ƙamshi. Gamal Eid shine darekta wata cibiyar yaɗa labarai dake Kairo.

US-Präsident Barack Obama und der ägyptische Präsident Hosni Mubarak

Barack Obama da Hosni Mubarak

"Batun Palasɗinawa yana daga cikin abinda yafi damun Larabawa a duniya. To amma akwai wasu matsalolin daban, misali ƙara yaɗuwar tsarin wahabiyanci, da kuma cin hanci da rashawa. Batun mulkin ɗimokraɗiyya baya cikin jadawali, 'yancin faɗar albarkacin baki, shima ba'A ambatonsa , ko kuma zaɓe mai adalci, duk waɗannan an lulluɓesu da batun mamayar Isra'ila"

Wani kyakkewan misali a wannan batun Palasɗinawa da Isra'ila shine batun ƙasar Misira, wanda ta rufe iyakar ta da Gaza, a wani mataki na hana shigar da makamai ga ƙungiyar Hamas dake iko da yankin. Don haka a zahiri batun cin mutuncin da Isra'ila take yiwa Palasɗinawa babu shi, kamar yadda yake shekaru 20 da suka gabata.

Mawallafa: Usman Sheh Usman da Hassan Znined

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal