1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau take Sallah a Nigeria da Niger

October 11, 2007
https://p.dw.com/p/Bu8i

A yau alúmar musulmi a ƙasashen yammacin Afrika suke gudanar da shagulgulan sallah karama bayan kammala azumin watan Ramadana. A Nigeria mai martaba sarkin musulmi kuma shugaban majalisar alámuran musulunci Alhaji Saád Abubakar na uku, a daren jiya ya sanar da ganin watan shawwal wanda ya kawo ƙarshen azumin na Ramadana. A saboda haka mai martaba Saád Abubakar ya umarci ɗaukacin musulumi a faɗin ƙasar su gudanar da sallar idi a yau Alhamis. A Jamhuriyar ma a yau ne musulmi a ƙasar suke gudanar da sallar idi bayan kammala azumin na Ramadana.