1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau take ranar dimokradiyya a Najeriya

Yusuf Bala Nayaya
May 29, 2017

Ranar dimokradiyya a Najeriya, ranar da ke zuwa daidai da cikar shugaba Buhari shekaru biyu a kan karagar mulki ya kuma fita daga kasar zuwa Birtaniya don neman lafiya.

https://p.dw.com/p/2dj3t
Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Akwai dai mabanbantan ra'ayoyi game da kamun ludayin shugaba Muhammadu Buhari kan muhimman batutuwa da suka hada da tsaro da tattalin arziki. Yayin da ake wannan biki na ranar ta dimokradiyya a gobe Talata kuma a kasar ake tuna shekaru 50 na masu fafutika ballewar Najeriya don kafa yankin Biafra, fafutikar da ta kai ga jefa kasar yanayi na yakin basasa, sai dai wannan lokaci na zuwa a daidai da lokacin da ake samun sabbin kiraye-kiraye na rajin kafa kasar ta Biafra inda 'yan fafutika daga Kungiyar (IPOB) da ta  (MASSOB) ke kiran wannan rana a matsayin ranar tuna baya.