1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

YAu ne wa´adin ƙarshe da komitin sulhu ya ba Iran domin yin watsi da batun nuklea

August 31, 2006
https://p.dw.com/p/Bul4

Yau ne wa´adin ƙarshe da komitin sulhu an Majalisar Dinkin Dunia ya ba Iran na ta yi wasti da batun ƙera makaman nuklea.

Saidai ya zuwa yanzu, ƙasar , ba ta da alamun cika wannan umurnin duk kuwa, da matsin lambar da ta ke fuskanta daga ƙasashen Amurika da turai.

A taron manema labarai da ya kira ranar talata da ta gabata, shugaban ƙasar Mahamud Ahmadinejdad, ya jaddada aniyar ƙasar sa, ta komawa tebrin shawarwari domin samun bakin zaren warware wannan taƙƙadama.

Tunni ne dai, Amurika ta yi barazanar ɗaukar matakan da su ka dace, idan a ka wuce ranar yau , ba tare da Iran ta bada kai bori ya hau ba.

Saidai ƙasashen Rasha da Chine, har yanzu na kan matsayin su, na adawa da matakan karya tattalin arziki, da Amurika ke bukatar komitin sulhu ya ɗauka a kan Iran.

Jikadan ƙasar Ghana, da ke jagorantar komitin sulhu a halin yanzu, ya sanar cewa, akwai wuya, a ɗauki irin wannan mataki cikin gaggawa.