Yau ne ranar yan gudun hijira ta duniya | Labarai | DW | 20.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ne ranar yan gudun hijira ta duniya

A yau ne Majalisar Dinkin Duniya take bikin ranar yan gudun hijira ta duniya,tana mai nuni da halinda yan gudun hijira fiye da miliyan 20 a duniya suke ciki.

Sakataren majalisar Kofi Annan yace nauyi ne daya rataya a wuyan dukkan alummomin duniya na kula da wadanda aka tilasatawa barin gidajensu.

A nashi bangare ministan harkokin cikin gida na Jamus, Wolfgang Schäuble yayi kira ne da daukar kwararan matakai na mayarda yan gudun hijirar kasashensu.

Schäauble yayi gargadin cewa,dole ne kasashen duniya su yaki dukkan wani abu da zai janyo halin gudun hijira,wanda yace yin hakan zai kuma taimaka wajen rage fataucin mutane musamman a nahiyar Afrika.