Yau ce ranar yaƙi da HIV/AIDS a duniya | Labarai | DW | 01.12.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ce ranar yaƙi da HIV/AIDS a duniya

Gwamnatoci a fadin duniya sun duƙufa wajen shawo hankali ga cutar HIV/AIDS .

default

Alamar cutar HIV/AIDS

Yau ce ranar yaƙi da cutar HIV/AIDS a duniya inda gwamnatoci ke ƙoƙarin shawo hankalin jama'a ga ƙwayar cutar HIV/AIDS mai karya garkuwar jiki. A dangane da haka ne aka haskaka muhimman wurare, kama daga dandalin Trafalgar da ke birnin London zuwa ginin Empire State da ke birnin New York, da launin ja da ke zaman alamar wannan cuta. A jiya da yamma ne dai aka fara tarbon ranar yau da haskaka zauren wasannin Opera House da ke birnin Sydney na ƙasar Australiya da jajayen fitillu. A cewar Ƙungiyar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kula da HIV/AIDS wato UNAIDS, kimanin mutane miliyan 33 da dubu 400 ne ke ɗauke da ƙwayar wannan cuta a duniya . A nan Jamus akwai kimanin mutane dubu 70 da suka kamu da wannan cuta. Kimanin mutane dubu uku ne kuma ke kamuwa da cutar a kowace shekara . Ƙwararru sun nunar da cewa duk da ci gaban da aka samu wajen samar da magungunan jiyar wannan cuta har yanzu ana ci gaba da nuna kyama da wariya ga masu ɗauke da ƙwayar cutar.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu