Yau ce ranar tunawa da yahudawan da ´yan Nazi suka yiwa kisan kiyashi | Labarai | DW | 27.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ce ranar tunawa da yahudawan da ´yan Nazi suka yiwa kisan kiyashi

A yau juma´a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag zata yi wani zama na musamman don tunawa da mutanen da ta´asar gwamnatin ´yan Nazi ta rutsa da su. MDD ce ta ware ranar 27 ga watan janeru na kowace shekara ta zama ranar tunawa da kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa a nahiyar Turai. A ranar 27 ga watan janerun shekarar 1945 sojojin rundunar Red Army suka ´yantad da dubban firsinoni da aka tsare a sansanin gwale-gwale na Auschwitz. A jawabinsa na wannan rana, babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira da a sa ido akan duk masu son su karyata aukuwar kisan kiyashin da aka yiwa yahudawa.