1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ce rana ta biyu kuma ta karshe a taron kolin kungiyar AU

January 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuSx
A yau talata ake kammala taron kolin yini biyu na kungiyar tarayyar Afirka a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha. A ranar farko na taron Sudan ta sha suka sannan an hana shugabanta Omar al-Bashir shugabancin kungiyar ta AU saboda ci-gaba da zubar da jini da ake yi a lardin Darfur dake yammacin Sudan. Maimakon haka an bawa shugaban Ghana John Kuffour shugabancin AU don haka ya dace da bukukuwan cika shekaru 50 da kasarsa ta samu ´yanci kai. A ranar 6 ga watan maris na shekara ta 1957 Ghana ta samu ´yancin ta daga Birtaniya. Mahalarta taron sun kuma mayar da hankali akan rikicin Somalia inda aka yi kira da a gaggauta girke sojojin Afirka a can.