1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ake maida hankali akan Darfur

September 17, 2006
https://p.dw.com/p/BujG

A yau ne ake sa ran masu fafutukar kare hakkin bil adama da shugabanin addinai a koina cikin duniya zasuyi zanga zanga da kuma taruka da nufin jawo hankulan jamaa game da halin da ake ciki a yankin Darfur na kasar Sudan.

A halin da ake ciki dai yanzu,shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya sake nanatawa sakataren Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan kin amincewarsa ga girke dakarun majalisar a yankin na Darfur da yaki yayi kaca kaca da shi.

A jiya asabar ne Firaministan Burtaniya Tony Blair yayiwa Sudan din tayin ihsani muddin dai ta kawo karshen rikicin na Darfur,amma in taki amincewa akwai yiwuwar lakaba mata takunkumi.