Yau ake janaizar Pierre Gemayel | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ake janaizar Pierre Gemayel

A yau ne ake janaizar ministan Lebanon Pierre Gemayel wanda wasu yan bindiga suka kashe a ranar talata.

Magoya bayansa sunyi kira dubban jamaa da su fito halartar wannan janaira wadda ake ganin zai iya rikedewa zuwa babbar zanga zanga kann titunan kasar.

Tun farko kafin kashe Gemayel kungiyar Hezbollah tayi barazanar gudanar da nata zanga zanga na kin jinin gwamnatin Fouad Siniora wanda Amurka ke marawa baya,amma jamian Hezbolla sun sanarda dakatar da zanga zangar har sai hankula sun kwanta bayan kashe Gemayel.

A halin da ake ciki kuma komitin sulhu na MDD ya baiwa masu bincike na majalisar umurnin taimakawa masu bincike na Lebanon wajen binciken kashe ministan.

Komitin sulhu ya yanke wannan shawara ce a jiya laraba bayanda sakatare Kofi Annan ya mika masu wata takarda dauke da bukatar taimakon majalisar daga firaminista Fouad Siniora.