Yau ake bukin cika shekaru 3 da kisan gillan yankin Beslan na Rasha | Labarai | DW | 01.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yau ake bukin cika shekaru 3 da kisan gillan yankin Beslan na Rasha

Mazauna yankin Beslan dake arewacin Ossetian na kasar Rasha sun yi addu´o´in tunawa da kisan gillan da aka yiwa wasu ´yan makaranta shekaru 3 da suka wuce. Mutane kimanin dubu 3 suka hallara a harabar makarantar don tunawa da wadanda wannan ta´asa ta rutsa da su. A ranar 1 ga watan satumban shekara ta 2004 ´yan awaren Chechniya suka yi garkuwa da mutane kimanin dubu daya a wannan makaranta. Kwanaki biyu bayan garkuwa mutane 332 daukacin su ´yan maranta sun rasu lokacin da sojojin kundunbala na Rasha suka farma ginin.