1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yau ake bude taron kungiyar taraiyar Afrika

January 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuSz

A yau ne ake bude taron kungiyar taraiyar Afrika AU a birnin Addis Ababa na kasar Habasha inda sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon ya shirya fuskantar kasar Sudan game da zargin da ake mata na take hakkin bil adama a yankin Darfur.

Neman tsayawa takara da shugaban sudan Omar al-bashir yayi na shugabancin kungiyar ta AU ya samu adawa daga wasu kasashe cikin kasashe 53 membobin kungiyar.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty tace kungiyar AU zata bata darajarta muddin dai ta zabi Sudan a matsayin shugabarta.

Gwamnatin Al Bashir dai ta karyata cewa tana marawa yan tawaye wadanda suka kwashe shekaru 4 suna aikata laifukan fyade,kawasar ganima da kashe kashe a darfur,haka zalika Sudan din har yanzu tana tababa game da aikewa da dakarun MDD zuwa Dafur.