Yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Brazil da Nijeriya | Labarai | DW | 30.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Brazil da Nijeriya

Kasashen Afirka sun nuna matukar sha´awa game da sabuwar fasahar samar da makamashi da ba ya gurbata yanayi. An jiyo haka ne daga bakin jakada Pedro Mota Pinto Coelho karamin minista a sashen Afirka da Asiya na ma´aikatar harkokin wajen Brazil. A wata hirar da tashar DW ta yi da jakadan wanda ke wakiltar Brazil a taron kolin kasashen Afirka da na Latunamirka a Abuja, ya nunar da cewa ana samun hadin kai a wannan fanni tsakanin kasashen Latunamirka kamar brazil da takwarorinsu na Afirka. Jakadan ya kuma yi tabo batun zirga-zirgar jiragen sama daga Nijeriya zuwa Brazil kai tsaye.

“Yanzu haka dai an kammala dukkan shirye shiryen sanya hannu kan yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakanin birnin Sao Paolo na Brazil da Legas na Nijeriya, wanda kamfanin Ocean Air na Brazil zai dauki nauyin sa. Ana kuma nazarin kulla irin wannan yarjejeniya da kasar Ghana.”