Yarjejeniyar zaman lahia tsakanin yan tawayen FNL da gwamnatin Burundi | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar zaman lahia tsakanin yan tawayen FNL da gwamnatin Burundi

A birnin Dar es-Salam, na ƙasar Tanzania, Gwamnatin Burundi, da yan tawayen FNL, sun rattaba hannu, a kan yarjejeniyar tsagaita wuta.

Wannan nasara, ta dasa aya, ga yaƙin bassasa, na tsawan shekaru 13, da ya galabaita ƙasar Burundi.

Shugaban ƙasar Tanazania, Jakaya Kikwete, da ya jagorancin tantanawar, yayi kira ga ɓangarorin 2, da su cika alkawuran da su ka ɗauka.

Shugaban ƙasar Afrika ta kudu, Tabon Mbeki, da Yuweri Museveni, na Angola, na daga shugabanin Afrika, da su ka halarci wannan biki.

An cimma wannan yarjejeniya, kwanaki 2 rak ,bayan da yan tawayen FNL su ka kai harin ,da yayi sanadiyar mutuwar mutan 1.

Kamin yarjejeniyar ta yau, FNL, itace ƙungiyar tawaye, ɗaya tilo, ta ƙi yin mubai´a ,ga shugaban ƙasa, Pierre Nkurunziza