Yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Somalia | Zamantakewa | DW | 23.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yarjejeniyar zaman lafiya a kasar Somalia

An cimma yarjejeniya sulhu tsakanin gwamnati da bangarorin adawa a Somalia

Halin rayuwar a Somalia

Halin rayuwar a Somalia

Batun samun zaman lafiya mai dorewa shi ne abun da alúmar kasar Somalia ke fatan ganin cimmawa, tun bayan barkewar rikici tsakanin gwamnati da yan adawa abin da kuma ya jawo hasarar rayukan jama masu dimbin yawa.

A ko ina dai a cikin kasar ta Somalia jamaá na ta jinjina yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin gwamnatin da yan adawar, ko hakan na iya kawo karshen fada da zubar da jinni a kasar wadda yaki ya daidaita.

A ranar alhamis din da ta gabata ce dai a taron sasantawa da kungiyar kasashen larabawa ta shiga tsakani a birnin Khartoum aka sami cimma yarjejeniyar tsakanin kotunan Islama da kuma gwamnatin ta Somalia.

Ko da yake yarjejeniyar wadda aka cimma a gaggauce bata sami warware batun rabon mukamai a gwamnatin ta hadin gwiwa ba, sai dai ta sami nasarar tsara kudirin tsagaita wuta domin kawo karshen fadan da yayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 360 da jikata wasu mutanen kimanin 2,000 a yan makwannin da suka gabata.

Taron na Khartoum shi ne shawarwarin shiga tsakani na farko da ya wakana tsakanin gwamnatin rikon kwaryar Somalia wadda bata da katabus da kuma kotunan Islama wadanda ke rike da mafi akasarin yankuna dake kudancin kasar wanda ya hada da babban birnin Mogadishu bayan fada mafi muni da baá taba ganin irin sa ba a kasar tun a shekarar 1991.

Da farko dai gwamnatin ta dauki kotunan islaman a matsayin kungiyoyin yan tarzoma wadanda ke kokarin dabbaka shariár musulunci a kasar yayin da a waje guda kuma kotunan islaman ke cewa shima shugaban kasar Abdullahi Yusuf Ahmed ba komai bane face madugun yaki.

A waje daya dai wasu alúmar kasar somalian na kallon yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanyawa hannu a birnin Khartoum a matsayin wata manufa ta samun tallafi na gudunmawar jin kai daga kasashen larabawa masu arzikin mai.Wani madugun yaki Abdi Ismail Guled na cewa wannan yarjejeniyar an yi tan e kawi domin dadadawa kasar Sudan wadda ta karbi bakuncin taron.

Shi kuwa wani malamin makaranta a birnin Mogadishu Abdulkadir Hassan cewa ya yi wannan ba wani abu bane face siyasa, domin kowa na son dalolin kudade daga albarkatun man petur. Yace to amma idan ana bukatar samun zaman lafiya tilas a yi amfani da karfi wajen tursasa bin umarni tare da aiwatar da yarjejeniyar da aka sanyawa hannu. Abdulkadir Hassan ya kara da cewa sun gaji da gafara sa basu ga kaho ba, sun kosa da jin cewa an sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiya, kana daga bisani a karya.

A nasa bangaren wani dan kasuwa Ahmed Muálim, yace ba za su dauki yarjejeniyar ta baya bayan nan da wani muhimmanci ba har sai sun ga an aiwatar da ita.

Majalisar dinkin duniya da kungiyar gamaiyar Afrika tare da kasar Amurka duk sun yi jinjina ga yarjejeniyar inda gwamnatin rikon kwaryar da kotunan islama suka amince da wanzuwar konen su.

Sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan ya baiyana yarjejeniyar da cewa babban mataki ne na cigaba.

Shi kuwa jakadan kungiyar gamaiyar Afrika a Somalia Mohammed Ali Foum yace nasarar cimma yarjejeniyar labari ne mai dadi ga samun daidaito da wanzuwar lumana a kasar Somalia musamman kasancewar bangarorin sun amince su dakatar da fada a junan su.

A yanzu dai bangarorin biyu sun amince da komawa teburin shawarwari a ranar 15 ga watan mai kamawa domin cimma masalaha a kan alámura da suka shafi shaánin tsaro.

Bayan samun nasarar kawar da madugan yaki kungiyar kotunan isalama ta yi kakkausar suka ga Amurka bisa danganta tad a tayi da kungiyoyin yan taádda tare da cewa tana bada maboya ga mayakan sa kai daga kasashen ketare.

Tuni yan islaman suka fara kakkafa kotunan yanki na shariár musulunci a yankunan dake karkashin ikon su.