yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Gwamnatin Uganda da yan tawayen LRA | Labarai | DW | 27.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Gwamnatin Uganda da yan tawayen LRA

bayan wata tsofuwar ƙungiyar tawaye.

Ranar talata ce mai zuwa, bakin ƙarhe 6 na sahe, yarjejeniyar da aka rattaba hannu kanta, tsakanin yan tawayen LRA, da gwamnatin Uganda ke fara aiki.

Ranar jiya assabar ɓangarorin 2, su ka cimma matakin kwance ɗamara yaƙi, a birnin Juba na kudancin Sudan,bayan shekaru kussan 19 na masanyar wuta.

Wakilin gwamnatin Uganda, bugu da ƙari, ministan cikin gida, ya bayana matukar farin cikin,da wannan matakin da a cimma, ya kuma yi kira ga ɓangarorin da su cika alkawuran da su ka ɗauka.

Kazalika, minista Ruhakana Rugunda, ya yi godiya ga hukumomin kudancin Sudan, a game da taimakon da su ka bada, na cimma tudun mun tsira tsakanin a rikicin tawayen Uganda.

A yayin da ya ke bayyani da sunan shugaban dakarun LRA, wakilin ƙungiyar tawaye a wannan taro,Obonyo Olweny ya alƙawarta mutunta yarjeneniyar, muddun ɓangaran gwamnati, bai saɓa nasa alƙawari ba.