Yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin zirin Gaza | Siyasa | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin zirin Gaza

Shugabanin Israila dana Falasdinawab sun cimma daidaito na kawo karshen musayar wuta a zirin Gaza

default

Shugabanin Falasdinawa dana Israila sun jaddada kudirin su na martaba yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin zirin Gaza. Sai dai kuma a waje guda yayin da yarjejeniyar ta fara aiki a yau litinin an ruwaito wasu Palasdinawa biyu sun rasa rayukan su a wani farmaki da sojin Israilan suka kai a kusa da garin Jenin dake gabar yamma da kogin Jordan.

A jiya lahadi harin rokar da yan takifen Palasdinawa suka kaiwa yankin Bani yahudu ya so ya raunana yarjejeniyar tsagaita wutar wanda aka cimma tsakanin mahukuntan Palasdinawa dana Israila. Ko da yake harin rokar wanda ya fada garin Sderot bai yi wani mummunan taádi ba, P/ M Palasdinawa Ismaila Haniya da shugaba mahmoud Abbas duk sun yi Allah wadai da harin wanda suka ce bai dace ba. A nasa bangaren P/M Israila Ehud Olmert yace ya umarci sojojin sa su nuna hakuri da juriya. Olmert yace yana da kwakwarar zaton zaá fadada yarjejeniyar tsagaita wutar ta hada da yankin gabar yamma.

Yarjejeniyar dai ta tanadi cewa idan yan takifen Palasdinawan suka daina kai harin rokoki, ita kuma Israila za ta janye sojojin ta daga Gaza.

Wata mai magana da yawun sojin Israilan yace, sojojin sun kammala janyewa daga yankin na Gaza da sanyin safiya.

Wani jamií a gwamnatin Palasdinawa Ibrahim Abu al-Naja wanda ke shugabantar kwamitin kungiyoyin Islama yace sun cimma daidaito na tuntubar juna tare da samar da wani managarcin shiri da zai karfafa alaka da zaman lafiya tsakanin su da Israila. Ya shaidawa manema labarai cewa an kafa kungiyoyi da za su sa ido domin cimma wannan manufa.

Shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas wanda tun da farko yayi Allah wadai da harin rokar da yan takife suka kai ya umarci tura jamián tsaron yankin zuwa arewacin zirin Gaza domin dakatar da irin wadannan hare hare da kuma martaba yarjejeniyar tsagaita wutar.

Shi ma P/M Ismaila haniya bayan ganawa da shugabannin kungiyoyi, ya yi kira a gare su, su taimaka wajen ganin baá karya yarjejeniyar ba, wadda dukkan bangarorin suka amince da ita.

Kungiyar ta Jihadil Islami ta ce ta kai harin rokar ne saboda farmakin da Israila ta cikin dare a gabar yamma. P/M Haniya yace zaá gudanar da bincike domin gano musabbabin wannan hari. Sai dai kuma kungiyar sojin Islama daya daga cikin kungiyoyi uku da suka yi garkuwa da sojin Israila wanda ya haddasa dauki ba dadi har tsawon watanni biyar tsakanin Israila da palasdinawa ta ce bata amince da yarjejeniyar da aka cimma ta tsagaita wuta ba.

An dai cimma yarjejeniyar tsagaita wutar ce a wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas da P/M Israila Ehud Olmert, a cewar kakakin gwamnatin Palasdinawan Nabil Abu Rudeina.

Amurka ta yi maraba da yarjejeniyar tsagaita wutar wadda ta ce babban mataki ne na dorewar zaman lafiya. Kakakin fadar Amurka ta White House Alex Conant yace suna fata hakan zai kawo raguwar tarzoma da tashe tashen hankula tsakanin alúmomin Israila dana Palasdinawa.

Palasdinawa kimanin 400 ne da sojin Iraila uku suka rasa rayukan su tun bayan da sojin Israilan suka kaddamar da farmaki a watan Junin da ya gabata domin dakatar da hare haren rokoki da kuma kwato sojin su da yan takifen Palasdinawan suka yi garkuwa da shi.