Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza | Labarai | DW | 27.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugabannin Israila dana Palasdinawa sun baiyana yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza da cewa zai samar da babbar daira ta tattaunawar zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu. An cigaba da aiwatar da yarjejeniyar a rana ta farko duk da harin rokoki da yankin na Gaza zuwa cikin Israila yan saoi bayan cimma tsagaita wutar. Kungiyar Hamas da ta Jihadil Islami sun ce su ke da alhakin wannan hari. P/M Israila Ehud Olmert yace ya umarci kwamnadojin sojin kasar su nuna hakuri da juriya. A waje guda kuma takwaran sa na yankin palasdinawa Ismaila Haniya yace dukkan bangarori a yankin sun yi alkawarin dakatar da hare haren rokoki zuwa yankin na Bani yahudu. Yayin da ita kuma Israilan ta amince ta janye sojojin ta daga Gaza.