yarjejeniyar sulhu tsakanin yan tawayen gabacin Sudan da gwamnati
June 20, 2006A yammacin jiya ne, babbar jama´iyar Sudan mai riƙe da ragamar mulki ta ƙaddamar da wani taron gangami abirnin Khartum, wanda ya samu halartar shugaban kasa Omar El beshir.
A cikin jawabin da ya gabar, Omar El Beshir, ya bayyana gamsuwa da yarjeniyoyi daban-daban,da a ka cimma tsakanin yan tawaye, da gwamnati.
An shirya taron, ranar da yan tawayen gabacin ƙasar da gwamnati su ka amice da tsagaita wuta, bayan wata da watani na tantanawa.
Saidai a wani sashen kuma, shugaban ƙasar Sudan, ya jaddada matsayin gwamnatin sa, na yin watsi da batun tura dakarun shiga tsakani,na Majalisar Ɗinkin Dunia a yankin Darfour.
Ya ce, yayi rantsuwa da mahallici , muddun ya na bisa karagar mulkin Sudan, babu batun aika tawagar Majalisar Sinkin Dunia a Darfour, domin,Soudan itace ƙasar farko a kudancin Sahara da ta samu yanci, daga turawan mulkin mallaka,a yanzu kuma, ba zata amince ba, ta koma ƙarkashin wanni saban mulkin mallaka inji shugaba El Beshir.