1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yarjejeniyar nukiliya tsakanin Indiya da Amurka

Amurka ta kulla yarjejeniyar taimaka wa Indiya da fasahar nukiliya

Watakila dai abu mafi alheri a wannan halin da muke ciki shi ne a yi gyara ga kudurorin yarjejeniyar hana yaduwar fasahar makaman nukiliya ko kuma a soke yarjejeniyar ma baki daya. Domin kuwa Amurka, wadda take daya daga cikin kasashen dake ba da cikakken goyan baya ga yarjejeniyar, ga alamu ba ta dauki lamarin da muhimmanci ba, musamman ma idan yayi daura da bukatunta. In kuwa ba haka ba, mene ne dalilin da zai sanya shugaba Bush ya cimma yarjejeniya da kasar Indiya, wacce ba ta da hannu a yarjejeniyar hana yaduwar fasahar makaman nukiliya, tare da doki da murnar cimma abin da ya kiwa wai sabuwar manufa ta kawance. Ko shakka babu a game da cewar kasar Indiya na bukatar makamashi kuma tashar nukiliya ka iya zama ginshikin wutar lantarki a kasar. Amma fa a daya bangaren Indiya na mallakar makaman kare dangi, lamarin da a zamkanin baya ya sha haddasa dardar da damuwa. A shekara ta 1974 kasar Indiya ta dauki matakin farko na gwada makamanta na kare dangi, sannan daga bisani ita ma Pakistan ta bi sau. Kuma dukkan kasashen biyu har yau ba su da hannu a yarjejeniyar hana yaduwar fasahar nukiliya. A sakamakon haka gwamnatin Amurka ta ki ba su hadin kai a duk wani abin da ya shafi fasahar nukiliya. A saboda haka ya zama abin mamaki yadda kasar ta Amurka ta canza alkibla tana mai ba wa kasar Indiya hadin kai duk da cewar bata da hannu a wannan yarjejeniya. Amma fa a fakaice akwai wasu dalilai da suka sanya Amurka ta fuskanci wannan sabuwar alkibla. Wadannan dalilai kuwa sun shafi kasar Iran. Ita Amurka kokarinta a nan shi ne ta janyo hankalin kasar Indiya da janye daga wani gagarumin shiri na na dasa bututan gas tsakanin Indiya da Iran, wanda zai ci dubban miliyoyi na dalar Amurka. Kawo yanzun dai Indiya ba ta ba da kai bori ya hau ga matsin lambar daga Amurka ba, amma tana amfani da sabanin dake akwai tsakanin Amurkan da Iran domin cimma bukatunta. A yanzu abin tambaya a nan shi ne, shin ta yaya Amurka zata ci gaba da neman goyan baya a adawarta da shirin Iran na nukiliya, kasar dake da hannu a yarjejeniyar hana yaduwar fasahar makaman kare dangi, sannan a lokaci guda tana rufa wa kasar Indiya baya ba tare da wata rufa-rufa ba? A wannan karon ma dai babbar daular ta duniya ta fito fili tana mai cin karenta babu ba babbaka kuma ba wanda ya ce mata uffan, abin da ya hada har da kawayenta na nahiyar Turai. Take-taken Amurka dai na mai yin nuni ne da cewar fadar mulki ta White House tana ba da la’akari ne kawai ga maslaharta, amma ba abin dake ci mata tuwo a kwarya a game da tsarin mulkin kasar da lamarin ya shafa. A takaice dai bisa ga dukkan alamu, ko ba dade ko ba jima, duniya zata wayi gari, an sa kafa an yi fatali da yarjejeniyar ta hana yaduwar fasahar makaman nukiliya.