1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar makamashi tsakanin Jamus da arewacin Najeriya

July 19, 2012

Jihohin Sakkwato, Kano, Bauchi da Katsina suka ƙulla yarjejeniyar samar wa jihohin wutar lantarki a ƙarƙashin wani shiri na kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamus.

https://p.dw.com/p/15aun
Die Kollektorenfläche eines solarthermisches Kraftwerks der Solar Millenium AG steht in Kalifornien (undatiertes Foto). In gleicher Bauweise wird das weltweit größte Solarkraftwerk im südspanischen Aldeire unter deutscher Regie entstehen. Der Grundstein für das 300 Millionen Euro teure Projekt "Andasol 1" wurde am Donnerstag (20.07.2006) gelegt. Innerhalb von zwei Jahren wird eine Kollektorfläche von mehr als 510.000 Quadratmetern installiert. Mit zirka 179 Gigawattstunden pro Jahr sollen rund 200.000 Menschen mit Strom versorgt werden. Das solarthermische Kraftwerk ist eine Entwicklung der Erlanger Solar Millenium AG. Im Gegensatz zu Photovoltaik-Anlagen, die elektrische Energie direkt aus Sonnenlicht gewinnen, erzeugen solarthermische Kraftwerke Strom aus der Wärmeenergie der aufgefangenen Sonnenstrahlen. Foto: Solar Millenium AG (zu dpa 0346) +++(c) dpa - Report+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Wani kamfanin ƙasar Jamus ne zai yi aiki samar da wutar lantarki da take da ƙaranci a Najeriya. Jamus dai ta ƙware a afashar saamar da wutar lantarki ta amfani da hasken rana.

Jihar Bauchi dake a arewa maso gabacin Najeriya na daga cikin jihohi da za ta ci gajiyar wannan fasaha ta samar da wutar lantarki ta hanyar hasken rana, wanda kampanin ƙasar ta Jamus mai suna Siemens zai aiwatar cikin watanni goma sha takwas masu zuwa.

Samar da wutar lantarki ta hasken rana a wasu jihohin arewacin Najeriya da suka haɗa da Sakkwato, Kano, Katsina, Bauchi da babban birnin tarayya ya biyo bayan wata yerjejeniya da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya shiga tsakani aka kulla tsakanin Najeriya da Jamus, wanda kuma aka kafa harsashin farko a Bauchi wadda za ta fara cin gajiyar wannan shiri.

An gudanar da kafa harsashin wannan shiri a gaban jakadiyar Jamus Dr. Dorothee Janetzke da jakadan Najeriya a Jamus Alhaji Abu Abubakar.

A cewar jakadiyar Jamus a Najeriya, dangantakar Najeriya da Jamus ba wani sabon abu ba ne, wannan dangantaka ta sa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta zo Nigeria shekarar da ta gabata, inda a nan ne aka yi maganar samar da wutar lantarki ta hasken rana wanda kuma ake fatan cewa bama yanzu ba harma 'ya'ya da jikoki za su ci gajiyar wannan shiri wanda kampanin Siemens zai yi.

P1050160 Funktionstest von Solarsystem st 2 (35 Euro), Im Hintergrund wird ein Handy geladen. bt Copyright: Stiftung Solarenergie, Fotograf: York Ditfurth Uneingeschränktes Verwertungsrecht für die Deutsche Welle Weitere Stichwörter für die Suche (bitte eingeben): Solar Solarenergie PV Äthiopien Sonnenenergie ländliche Elektrifizierung Kerosien LED
Hasken wutar lantarki da ƙarfin rana a yankunan karkaraHoto: Stiftung Solarenergie

Ta ce kamfanonin Jamus wanda yanzu haka suke cika shekaru hamsin suna aiki a Najeriya, ta ƙara cewa tana yiwa al'ummar jihar Bauchi fatan alheri wadda ita ce ta farko da za ta ci gajiyar wannan shiri, wanda za'a iya gani a ƙasa zahiri ba badili ba a yerjejeniyar tsakanin ƙasashen biyu.

Shi kuwa gwamnan jihar Bauchi Mallam Isa Yuguda, dake cike da murna, cewa yayi wannan abin alfahari ne ga al'ummar jihar Bauchi, ya ce kamfanonin Jamus da za su aiwatar, bama wannan ba harma da sauran alfanu.

Mawallafi: Ado Abdullahi Hazzad
Edita: Mohammad Nasiru Awal