1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kulla gwamnatin kawance a tarayyar Jamus

November 12, 2005
https://p.dw.com/p/BvLP

Shugabannin manyan jam´iyun siyasa a nan Jamus sun bayyana abubuwan dake kunshe cikin wata yarjejeniyar da suka cimma da nufin kafa wata babbar gwamnatin kawance karkashin jagorancin mai ra´ayin mazan jiya Angela Merkel. A lokacin da take magana a gaban wani taron manema labarai shugabar gwamnatin Jamus mai jirar gado Angela Merkel ta ce babbar manufar yarjejeniyar shi ne kirkiro sabbin guraben aiki a Jamus tare da daukar managartan matakan ta da komadar tattalin arzikin kasar. A jiya da daddare shugabannin jam´iyun Christian Democrats ta ´yan ra´ayin mazan jiya da na Social Democrats suka cimma yarjejeniyar wadda ta kawo karshen dambaruwar siyasar da aka shafe makonni 8 ana yi bayan zaben ´yan majalisar dokoki wanda ba jam´iyar da ta samu gagarumin rinjaye da ake bukata don kafa gwamnati ba. Dole ne dai a amince da ka´idojin yarjejeniyar a gun babban taron da kowace jam´iya dake cikin gwamnatin zata yi a farkon mako mai zuwa.